Mu ƴan arewa ba mu ga alkairin gwamnatin Tinubu ba - Dalung

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Mu ƴan arewa ba mu ga alkairin gwamnatin Tinubu ba - Dalung

Tsohon ministan matasan Najeriya kuma ɗan gwagwarmaya, Barista Solomon Dalung ya ce a tsawon shekaru biyu na mulkin shugaba Tinuba mutanen arewacin Najeriya ba su ga komai ba.

"Ban da yunwa da rashin tsaro babu wani abu da ƴan arewacin Najeriya za su iya bugun ƙirji su ce sun samu a ƙarƙashin gwamnatin nan." In ji Solomon Dalong.

Tsohon ministan ya ce idan dai har ana son a yi abin da ya kamata ga talakawa ƴan ƙasa to dole ne gwamnatin Tinubu ta "zauna ta yi tunanin mayar da tallafin man fetur da na wutar lantarki da ta janye".