... Daga Bakin Mai Ita tare da Gundura Zaria
A wannan makon za mu kawo muku ...Daga Bakin Mai Ita tare da Muhammad Lawan da aka fi sani da Gundura Zaria.
An haifi Muhammad Lawan Gundura a ranar 17 ga wata Agustan 1970, yayi karatunsa a Zaria, sannan ya je jami'ar Amadu Bello da ke Zaria.
Ya fara wasan kwaikwayo tun yana aji shida na Firamare. Kuma tun daga nan har yanzu ana damawa da shi.
Ya samo sunan Gundura tun yana jam'iar Ahmadu Bello da ke Zaria, saboda yadda mutanen suke matsa masa cewar ya takura musu, ya gundire su, daga nan ya sami sunan, kuma ya bishi.
Sannan ya zaɓi wasan kwaikwayo na ban dariya saboda sha'awa.
Cikin Fina-finan da ya yi suna sun hada da Gundura, Karan Batta sai kuma Lumbu-lumbu da makantansu.