Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ku ci gaba da kasancewa da shafinmu na intanet bbchausa.com da kuma sauran shafukanmu na sada zumunta domin samun labarai daban-daban har ma da sanin yadda za ta karkare tsakanin PSG da Inter.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
An tafi hutun rabin lokaci PSG na gaban Inter, PSG 2-0 Inter Milan
Asalin hoton, Getty Images
An tafi hutun rabin lokaci a fafatawa tsakanin PSG da Inter Milan a filin wasa na Munich Arena.
Zuwa yanzu dai ƙungiyar Paris wato PSG na gaban Inter da ci 2-0.
Akwai jan aiki a gaban Inter idan har tana son dawowa cikin wannan wasa.
A ɗaya gefen kuwa, saura mintuna 45 PSG ta lashe kofin Zakarun Turai karon farko a tarihinta.
Shin wane yanayi magoya bayan Inter ke ciki a Italiya?
Magiya bayan Inter Milan da ke kallon wasan karshe na gasar Zakarun Turai da ƙungiyarsu ke buga wa sun kaɗu matuka da yadda wasan ke tafiya.
Ɗimbin magoya baya sun yi jigum fuskokinsu a murtuke, alamu da ke nuna cewa ba su gamsu da salon wasan da Inter ke yi ba zuwa yanzu.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Hamas ta yi martani ga tayin Amurka na kawo karshen yaƙin Gaza
Asalin hoton, Reuters
Hamas ta yi martani ga tayin Amurka na kawo karshen yaƙi a Gaza.
Ƙungiyar ta amince za ta saki mutum goma waɗanda ta yi garkuwa da su tare da gawawwaki 18 cikin, a matsayin musayar Falasɗinawan da Isra'ila ke tsare da su.
Sannan Hamas ta sake gabatar da wasu sharuɗanta da Isra'ila ta yi watsi da su, waɗanda suka haɗa da tsagaita wuta ta dindindin da kuma janyewar Isra'ila gaba-ɗaya daga Gaza.
Wakilin BBC ya ce martanin Hamas ɗin ya yi kama da rashin amincewa da buƙatar jakadan Amurka Steve Witkoff amma cikin diflomasiyya.
PSG 2-0 Inter Milan
Asalin hoton, Getty Images
Desire Doue ya ci wa PSG kwallo ta biyu.
Kwallo ce mai kyau ya ci a cikin yadi na 18.
Yanzu dai Inter na da jan aiki a gabanta idan tana son dawowa cikin wannan wasa.
PSG ta zura wa Inter kwallo ɗaya, PSG 1-0 Inter Milan
Asalin hoton, Getty Images
PSG ta samu damar zura kwallo ɗaya a ragar Inter Milan.
Achraf Hakimi ne ya ci kwallo mai kyau a minti na 12.
Sai dai bai yi wata murna ba inda ya ɗaga hannun sama, kasancewar Inter tsohuwar ƙungiyarsa ce.
An rantsar da Kamil al-Tayeb sabon Firaministan Sudan
Asalin hoton, Getty Images
An rantsar da tsohon jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya, Kamil al-Tayeb Idris, a matsayin sabon Firaministan Sudan a birnin Port Sudan.
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Susan ne Janar Abdel Fattah al-Burhan ya naɗa mista Idris a kan muƙamin.
Ya zama sabon Firaminista tun bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da gwamnatin farar-hula ta Omar al Bashir a shekara ta 2021.
Ana sa ran zai kafa muƙarrabai a daidai lokacin da sojojin ƙasar ke ci gaba da faɗa da dakarun RSF.
Ma'aikatar lafiya karkashin ikon Hamas a Gaza, ta ce an kashe Falasɗinawa 60 tare da jikkata wasu 284 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
A cikin bayanai da ma'aikatar ke fitar wa, ta ce alkaluman ba su kunshi na asibitocin da ke arewacin zirin Gaza ba saboda wahala wajen kai wa yankin.
Wannan ya kawo alkaluman waɗanda suka mutu tun soma yaƙin ranar 7 ga Oktoban 2023 zuwa mutum 54,381. An kuma jikkata 124,054.
Isra'ila ta fara farmakin soji kan Gaza ne a matsayin martani ga harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga Oktoban, 2023 - inda aka kashe mutum 1,200.
Ba za ku so wasan karshe na Zakarun Turai ya wuce ku ba
Asalin hoton, Getty Images
Wasan karshe na gasar Zakarun Turai, babban wasa ne a kololuwar kwallon kafa a Turai, inda ƙungiyoyin PSG da kuma Inter Milan ke son lashe gasar ta bana.
Paris St-Germain ba ta so a riƙa tuna mata cewa ba ta taɓa lashe gasar ba, yayin da Inter kuwa ta shafe shekara kusan 15 ba tare da ɗaukar kofin ba - lokaci na karshe da ta yi nasarar daukarsa shi ne 2010.
Dare mai farin ciki na jiran ɓangare ɗaya, sannan baƙin-ciki da hawaye ga guda.
Shin wace ƙungiya ce za ta samu nasarar zama zakarun Turai idan anjima? Lokaci ne kawai zai fayyace hakan.
Iran ta haramta kallon shirin 'Suvushun' mai dogon zango
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a ƙasar sun haramta wata manhajar kallon fina-finai daga nuna wani mai fim mai 'Suvushun' saboda yana "ƙunshe da abubuwa da suka saɓa wa addinin musulunci".
Gwamnatin ta ce a cikin shirin wanda mai dogon zango ne akwai wuraren da ake nuna mata da maza suna rawa a tare, sannan wasu waɗanda suka fito a mata da miji suna taɓa juna, wanda hukumomin ƙasar suka ce "haramun ne a dokokin shari'ar musulunci a ƙasar."
Hukumar kula da kafofin sadarwa ta ƙasar ta ce shirin ya saɓa dokokin watsa labarai na ƙasar, kuma ya karya dokokin samun lasisin haska fim a ƙasar.
Sai dai manhajar ta Namava ta nuna rashin amincewa da hukuncin, inda ta ce sai da ta samu lasisi kafin ta fitar da shirin.
Masu ra'ayin riƙau na ƙasar sun yaba da matakin, inda suke cewa hakan zai taimaka wajen 'kare al'adun ƙasar'
Dubban magoya baya sun fara hallara a Munich don kallon wasan karshe na Champions League
Asalin hoton, Getty Images
Dubban masoya kwallon kafa ne suka fara hallara a filin wasa na Munich domin kallon wasan karshe na gasar Zakarun Turai.
Parist St-Germain ta Faransa za ta fafata da Inter Milan ta Italiya, inda kowannensu ke ƙoƙarin ganin ya lashe kofin.
PSG ba ta taɓa lashe kofin ba a tarihinta duk da kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen ƴan wasa a shekarun da suka gabata - Inter Milan ta lashe gasar har sau uku.
Ana sa ran mutum 70,000 ne za su kasance a filin wasan Munich Allianz Arena, inda miliyoyi kuma daga sassan duniya za su kalli wasa a gidajen talbijin.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Ambaliyar Neja: Ana ci gaba da aikin zaƙulo gawawwaki
Asalin hoton, Reuters
Hukumomi a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya, sun ce ana ci gaba da aikin ceto bayan ambaliya ta lalata gidaje da kuma gadoji da dama a jihar.
An ruwaito mutuwar mutum sama da 150, tun bayan afkuwar ambaliyar a garin Mokwa sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi ranar Laraba da daddare.
Har ta kai sai da aka kai kogin Neja domin gano wasu gawawwaki.
Lamarin ya ɗaiɗaita dubban mutane, inda mutane ke fama da matsalar abinci da kuma ruwan sha.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, ta ce waɗanda suka samu raunuka na ci gaba da samun kulawa yayin da aka rarraba kayan agaji ga waɗanda lamarin ya shafa.
Amurka ta zargi China da yunƙurin mamaye yankin Taiwan
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren
tsaron Amurka Pete Hegseth ya zargi China da neman sauya al'amura a yankin
Indiya da Pacific, ta hanyar fara shirin mamaye yankin Taiwan.
Yana magana
ne a wani babban taron tsaro da aka gudanar a Singapore, inda ya ce Beijing na
neman mamaye yankin, amma Amurka ba za ta naɗe ƙafa tana kallo hakan ta faru
ba.
Ya ce ba ma
neman rikici da China, ba za mu yi wani abu na tunzuri ko aibata China ba,
shugaba Trump na mutunta al'ummar China, amma kuma ba za mu bari a kore mu daga
wannan yanki mai muhimmanci ba.
Mista
Hegseth ya yi kira ga ƙawayen Amurka na yankin da su taka tasu rawar ta hanyar ƙara abun da suke kashewa a ɓangaren tsaro don kare kansu daga China.
Mutum 19 sun rasu bayan tawagar ƴanwasan Kano sun yi hatsari
Asalin hoton, Gwamnatin Kano
Motar da ke ɗauke da ƴanwasan Kano da masu horar da su a gasar wasanni ta ƙasa wato National Sport Festival ta Najeriya ta yi hatsarin a hanyar komawa gida, inda rahotanni suka ce mutum 19 daga cikinsu sun rasu, sannan wasu sun jikkata.
Lamarin ya faru kimanin kilomita 50 zuwa Kano a yau Asabar bayan motar ta taso daga jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar bayan an kammala wasannin a ranar Juma'a.
Ibrahim Umar Fage shugaban riƙo na hukumar wasanni ta jihar Kano ya tabbatar wa BBC da aukuwar lamarin, inda ya ce, "ƴanwasanmu sun kwana a Abuja ne da safe sai suka kama hanyar komawa gida. A kusa da Dakatsalle suka yi hatsari. Motar ta faɗa wata gada da ke kusa da Ciromawa. Aƙalla mutum 19 zuwa 20 ne suka rasu, akwai wasu kuma a asibiti," in ji shi.
Shi ma Kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya bayyana kaɗuwarsa kan hatsarin, inda ya ce lamari ne da ya taɓa jihar baki ɗaya.
A wata sanarwa da kwamishinan ya fitar, ya ce "wannan lamarin abin tayar da hakali ne matuƙa. Muna jajanta wa ƴanuwa da iyalan waɗanda suka rasu da ma mutanen jihar Kano baki ɗaya," in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ɗauki ɗawainiyar kula da sauran waɗanda suka ji raunuka.
Waɗanda suka rasu a ambaliyar Neja sun kai 151
Asalin hoton, Adamu Ngulde
Bayanan hoto, Wata ambaliya da aka yi a jihar Borno
Hukumomi a jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya sun ce waɗanda suka rasu a ambaliyar ruwa da ta dabaibaye yankin Mokwa na jihar sun kai 151 zuwa yanzu.
Ambaliyar wadda ta fara a sanadiyyar mamakon ruwan sama da aka yi a ranar Laraba, ta yi sanadiyar raba sama da mutum 3000 da muhallansu.
Haka kuma ambaliyar ta ɗaiɗaita gidaje da gonaki da gadoji da titunan jihar.
Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ya shaida wa BBC cewa gidaje sama da 500 ne suka lalace.
Gwamnatin Sokoto ta amince da biyan albashin watan Yuni domin bukukuwan Sallah
Asalin hoton, Ahmed Aliyu
Gwamnan jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, Ahmed Aliyu ya amince da biyan ma'aikatan jihar albashin watan Yuni domin bukukuwan Babbar Sallah.
A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Abubakar Bawa ya fitar, ya ce gwamnan ya yi haka ne domin sauƙaƙa wa ma'aikatan jihar.
"Za a fara biyan albashin ne daga ranar Litinin, 2 ga watan Yunin domin ma'aikata da ƴan fansho na jihar su samu sukunin gudanar da shagulgulansu na Sallah cikin walwalwala."
"Sai dai ina sake kira ga ma'aikatan jihar da suma su mayar da biki wajen mayar da hankali kan aikinsu, kamar yadda muka mayar da hankali wajen lura da jin daɗinsu."
A ƙarshe Gwamna Aliyu ya nanata ƙudurin gwamnatinsa na cigaba da inganta aikin gwamnati da jin daɗi da walwalar ma'aikatan jihar, "sannan ina ƙara tabbatar wa mutanemu na jihar Sokoto cewa za su cigaba da ganin romom dimokuraɗiyya a ƙasa."
Isra'ila ta hana ministocin ƙasashen Larabawa taro a Gaza
Asalin hoton, AFP
Rahotanni na cewa gwamnatin Isra'ila ta hana ministocin harkokin ƙasashen Larabawa da dama shiga gaɓar yammacin kogin Jordan da ta mamaye domin wani taro a birnin Ramallah.
An tsara manyan jami'an diflomasiyyar Saudiyya da Jordan da Masar da Qatar da Turkiyya da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za su gana da shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas gobe Lahadi.
Sai dai Isra'ila ta ce ɗaukar wannan mataki ya zama dole, domin ta lura hukumomin Falasɗinawan na shirin yin amfani da ziyarar ne wajen farfaɗo da kiran samar da ƙasar Falasɗinawa.
Ƙasashen Larabawar sun yi ta ƙoƙarin ganin an tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce za a iya dakatar matsalar yunwar da ake fama da ita a Gaza, idan har an so yin hakan da gaske.
Shugaban hukumar tallafa wa Falasɗinawa ta MDD, Philippe Lazzarini, ya ce al'ummar Gaza na fama da yunwa a daidai lokacin da suke ta faɗi tashin tsira daga tashin bama-bamai.
Ya ce taimakon da ake aika wa yanzu daidai yake da izgilanci, domin duka-duka bai wuce kashi goma cikin 100 na abin da ake buƙata ba.
Ba tare da ambaton Isra'ila ba, Mista Lazzarini ya ce dole ne a bar Majalisar Ɗinkin Duniya da abokan hulɗarta su yi aikinsu da kuma taimaka wa masu buƙata.
Tun da farko hukumar jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Gaza, shi ne "wuri mafi fama da yunwa a duniya" inda dukkan jama'ar da ke yankin ke fama da matsalar.
Masana'antun China na samun koma-baya
Asalin hoton, EPA
Alaƙaluman hukuma sun nuna cewa ayyukan masana'antu na ƙasar China sun ragu a
wata na biyu a jere a cikin watan Mayu duk da cewa Beijing da Washington sun
amince su dakatar da rikicin kasuwancin da ke tsakaninsu, na tsawon kwana 90 a
farkon wannan watan na .
Ana dai
danganta wannan koma baya da rashin buƙatar kayayyakin ƙasar daga waje, da kuma
rashin fitar da su zuwa Amurkar sakamakon harajin da Amurka ta lafta wa China.
Sai da ta
kai harajin ya kai kashi 145 cikin 100, yayin da ita ma Beijing ta sanya wa
Amurkar harajin ramuwar gayya kan kayayyakinta da kashi 125%.
Champions League: Abubuwan da ba ku sani ba kan wasan Inter da PSG
Asalin hoton, Getty Images
A yau Asabar, 31 ga watan Mayu ne za a fafata wasan ƙarshe na gasar Champions League, wanda za a buga a filin wasan Munich Football Arena da ke Munich a ƙasar Jamus.
Za a ɓarje gumi tsakanin ƙungiyar PSG ta Faransa da Inter Milan ta Italiya, wanda kusan shi ne wasa babba da ake tsimayi a kakar wasan ƙwallon ƙafa ta bana wadda ake ƙarƙarewa.
Real Madrid ce ta lashe gasar ta kakar bara, inda ta doke ƙungiyar Dortmund ta Jamus da ci biyu da nema a wasan ƙarshe a filin wasa Wembley da ke birnin London na Ingila.