Mu kwana lafiya
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu zama lafiya.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/06/2025
Isiyaku Muhammed da Ahmad Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu zama lafiya.
Asalin hoton, Reuters
Ukraine ta kai wa yankunan Rasha mummunan hari irinsa na farko tun bayan mamayar da aka yi wa ƙasar.
An yi amfani da jirage marasa matuki wajen kai hare-haren, a kusa da birnin Moscow.
Ukraine ta ce ta tarwatsa jiragen yaƙi 41.
Wani jami'in hukumar leƙen asirin Ukraine ya ce an shigar da jirage marasa matukan cikin Rasha a wata motar dakon kaya, sannan aka binne su cikin rumfuna.
Daga bisani kuma aka buɗe rufin rumfunan daga nesa yadda jiragen suka samu damar fita su tashi sama.
An bayyana cewqa Ukraine na tsara kai harin tsawon watanni 18, wanda shugaba Zelensky ya jagoranta.
Moscow wadda ta tabbatar da faruwar hare-haren, ta ce biyu ne kawai suka yi nasara.
Asalin hoton, Reuters
Mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a garin Mokwa na jihar Neja sun kai sama da 200, in ji jami'ai.
Akwai wasu kusan 500 da ba a gani ba har yanzu, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Mataimakin shugaban karamar hukumar Mokwa, Musa Kimboku ya shaida wa BBC cewa an dakatar da aikin ceto saboda hukumomi sun yi imanin cewa watakila babu wanda ya rage da rai.
Ambaliyar wadda aka bayyana cewa ba a ga irinta ba tsawon shekara 60, ta lalata gidaje a anguwannin Tiffin Maza da Hausawa, bayan tafka mamakon ruwan sama ranar Laraba da daddare.
Hukumomi za su fara tono gawawwaki da aka binne don bincike, a wani yunkuri na kauce wa yaɗuwar cutuka, kamar yadda Maigarin Mokwa Muhammad Aliyu ya bayyana.
Mazauna yankin sun bayyana cikin kaɗuwa yadda suna kallo suka rasa ƴan uwansu da gidajensu bayan da ruwa ya tafi da su.
Wani mai suna Adamu Yusuf, ya ce ya rasa matarsa da kuma jaririnta.
"Ina ji ina gani har ruwa ya tafi da su babu yanda na iya. Na samu tsira ne saboda ina iya yin iwo," ya faɗa wa BBC.
Asalin hoton, Getty Images
Ministocin harkokin wajen ƙasashen Larabawa sun bayyana rashin jin daɗinsu ga gwamnatin Isra'ila, game da rashin amincewa da tawagar ƙungiyar ƙasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gaɓar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasɗinawa.
A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa'ud, ya ce matakin da Isra'ila ta ɗauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya.
A ranar Asabar wani jami'in Isra'ila ya ce batun samar da ƙasar Falasɗinu ne manufar ziyarar.
Cikin wata sanarwar haɗin-gwiwa, ƙasashen Masar da Qatar sun ce za su ruɓanya ƙoƙarinsu don a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Shugaban ƙungiyar ƙasashen Larabawa da ministoci huɗu sun gana da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ta kafar Intanet.
Asalin hoton, Getty Images
Dandazon magoya baya ne suka yi jerin gwano a titunan birnin Paris domin tarbar Paris St-Germain bayan lashe kofin zakarun Turai ranar Asabar.
Sabbin zakarun na Turai waɗanda suka hau motar bas cike da murna sun yi ta karaɗe tituna, inda daga bisani suka zarce fadar shugaban ƙasar don liyafar cin abinci da shugaba Emmanuel Macron ya shirya musu.
Sai dai, kafin komawarsu gida daga Jamus, na samu tarzoma daga magoya baya inda suka yi artabu da ƴansanda abin da ya kai ga kama ɗaruruwa har ma da mutuwar biyu.
Wannan ce karon farko da PSG ta lashe kofin a tarihinta.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Anadolu/Getty Images
Jami'ai a Falasɗinu sun ce aƙalla mutum 31 ne suka mutu bayan hari da Isra'ila ta kai kusa da wurin rabon abinci a birnin Rafah.
Jami'an lafiya sun ce sama da mutum 150 ne kuma suka jikkata.
Sai dai dakarun tsaron Isra'ila sun ce ba su da masaniyar ɓarnar da harin su ya yi a birnin ba, sannan wata gidauniyar jin-ƙai a Gaza ta musanta rahoton - inda ta ce Hamas ce ta kirkiro shi.
Rahotanni daga ɓangaren Falasɗinawa sun ce akwai irin wannan lamari a kusa wurin rabon kayan agaji a tsakiyar Gaza.
Shugaban hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da ƴan gudun hijirar Falasɗinawa, Philippe Lazzarini, ya ce rabon kayan agaji ya zama tarkon mutuwa.
Asalin hoton, NDLEA/X
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta ce ta gano 'gugun' masu shiga sahun alhazai don safarar hodar iblis zuwa Saudiyya.
Sanarwar da hukumar ta fitar ranar Lahadi, ta ce an kama mutanen ne a jihar Kano, bayan samun bayanan sirri.
Hakan kuma ya biyo bayan kama wasu alhazai biyu a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, lokacin da mahajjata ke shirin shiga jirgi zuwa Jeddah.
"An samu nasarar kama su ne a filin jirgin sama a Kano bayan samun bayanan sirri. Sakamakon bincike ya nuna sun haɗiye ƙwayoyin a cikinsu," in ji sanarwar.
Har ila yau, binciken ya gano cewa 'gungun' mutanen suna da wata ƙungiya da ta shahara wajen safarar ƙwayoyi zuwa Saudiyya.
Asalin hoton, Getty Images
An kama ɗaruruwan mutane sannan biyu sun mutu lokacin murnar nasarar Paris St-Germain a gasar Zakarun Turai a Faransa.
PSG ta lashe Champions League karon farko a tarihinta, bayan doke Inter Milan 5-0.
An cinna wa motoci sama da 250 wuta yayin da magoya bayan suka yi artabu da ƴansanda a faɗin ƙasar.
A wasu wurare, direbobi sun bi ta kan masu tafiya a ƙafa, inda har ta kai ɗaya ya mutu a Paris.
An kuma daɓa wa wani matashi wuƙa a garin Dax da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Har ila yau, an jikkata ƴansanda 18, inda aka saka wa ɗaya na'urar taimako wajen numfashi a yankin Normandy.
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar agaji ta Red Crestent da ke yankin Falasɗinu ta ce hare-haren tankokin yaƙin Isra'ila sun yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 23 tare da jikka wasu mutum 23 daga cikin masu aikin agaji a yankin Rafah da ke Gaza.
Haka kuma ƙungiyar ta ce ta kwashe wasu mutum 14 da suka samu rauni a wani wajen bayar da agaji a ke kusa da Netzarim da ke Gaza.
Ita kuma ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce waɗanda suka mutu sun kai 31, a daidai lokacin da rundunar tsaron Isra'ila wato IDF ta ce ita dai ta kai hari ne kan wasu ƴanta'adda a Khan Younis.
Sai dai kuma gidauniyar agaji ta Gaza Humanitarian Foundation ta aike wa BBC saƙo, inda a ciki ta ce duk labaran da ake yaɗawa ƙarye ne, babu wani harin da aka kai kan masu rabon kayan agaji.
Asalin hoton, Reuters
A yau ne al'ummar Mexico za su yi wani zaɓe irinsa na farko da za su zaɓi gabaɗayan ɓangaren shari'ar ƙasar ta hanyar kaɗa ƙuri'a.
Ƙasashe da dama da suka haɗa da Amurka da Switzerland da Bolivia suna da tsarin zaɓen alƙalai, amma wasu daga ciki kawai ake zaɓa, a naɗa wasu.
Sai dai a wannan yanayi da ba a taɓa gani ba, ita ƙasar Mexico za ta kasance ƙasa ta farko da za a zaɓi dukkanin alƙalanta - kama daga ƙanana har zuwa na na kotun ƙoli.
Asalin hoton, NAHCON/X
Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun gargaɗi mahajjata da ke ƙasar domin gudanar da aikin Hajji game da yanayi na matsanancin zafin rana da ake fuskanta a halin yanzu.
Akan haka ne ma Ma’aikatar aikin Hajji ta ƙasar ta umurci hukumomin alhazai na ƙasashen duniya a kan su ja hankalin maniyyata su guji yawace-yawace a cikin rana, inda ake hasashen yanayin zafin ka iya kaiwa maki 50 na Celsius musamman a ranar hawan Arfa.
Dokta Hamidu Liman, shi ne babban likita da ke kula da kiwon lafiyar alhazan Najeriya a Madinah, ya bayyana na BBC cewa lallai akwai zafi.
Ya ce ana sa ran za a kasance cikin zafin har zuwa ranar Arfa kuma zafin zai kai aƙalla 45 a ma'aunin celcius zuwa 50.
"Dama kowace shekara kan zo da nata yanayin daban. Yanzu ne lokacin zafi a Saudiyya, kuma yanayin zai iya yi wa mutum illa."
Sai dai ya a Madina da yake mutum uku ne suka suma saboda zafin, "amma an ba su taimakon farko kuma sun warware."
Asalin hoton, Reuters
Rahotanni daga Gaza na cewa Hamdi al Najjar, wani likita da aka kashe ƴaƴansa 9 cikin 10, sakamakon harin da Isra'ila ta kai mako guda da ya wuce, shi ma ya mutu, sakamakon munanan raunukan da ya samu a harin.
Matarsa Alaa al Najjar, wadda ita ma likita ce a asibitin Nasser da ke Khan Younis, ta tsira tare da yaronsu na goma wanda shi ma dai ya samu munanan raunuka.
Jiya Asabar, ma'aikatar lafiya ta Gaza, ta sa ce sama da mutum 4,000 ne Isra'ila ta kashe a yankin tun bayan da ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakiyar watan Maris.
A Najeriya masana lamuran tsaro na ci gaba da bayyana albarkacin baki kan samun jami'an tsaro da suke safarar makamai ga ƴanbindiga.
Masana suna cewa rashin ɗaukar matakan hukunta jami’an tsaron da aka samu da laifin safarar makamai ga ƴanbindiga, da kuma biyan jami’an tsaron ƙasar albashin da bai taka kara ya karya ba, na daga cikin abubuwan da ke taka rawa wajen ci gaba da samun karuwar wasu baragurbin jami’an tsaron da ke safarar makamai ga mayaƙan Boko Haram da ‘yan fashin daji.
Barista Audu Bulama Bukarti, lauya kuma masani lamuran tsaro ne a nahiyar Afirka, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Najeriya na sakaci da lamuran da suka shafi tsaro da suka haɗa da rashin bibiyar yadda ake kashe kuɗaɗe a ɓangaren da ma yin biris da makomar sojoji da sauran masu aikin samar da tsaro a kasar.
Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, ana ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar ruwan da ta auku a garin Mokawa na jihar Neja, inda ya zuwa yanzu aka gano sama da gawa 150, kuma akwai sauran fiye da 400 da ake nema, yayin da gwamnatin jihar Neja da hukumomi da kungiyoyin agaji ke ci gaba da kai dauki ga daruruwan mutane da ambaliyar ruwan ta shafa.
Kwamared Yakubu Garba, mataimakin gwamnan jihar Nejar, wanda ya kai ziyarar gani da ido da kuma jaje garin na Mokwa ne ya bayyana wa BBC hakan, inda ya ce lamarin akwai ɗaga hankali.
Ya ce, "Aƙalla akwai mutum 40 ba suka ɓace har yanzu ba a gansu ba kuma ba a gano gawarsu ba. Ana dai cigaba da nemansu."
Asalin hoton, FACEBOOK
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin ranar jimami a jihar, inda ya amince da ba ma'aikatan jihar hutun aiki domin alhinin waɗanda suka rasu daga cikin tawagar ƴanwasanta da suke yi hatsari a hanyarsu ta komawa gida daga wasannin ƙasa da aka yi a Ogun.
Zuwa yanzu dai inda mutum 22 suka rasu daga cikin tawagar ƴanwasan, sannan wasu kuma suka jikkata.
A sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya kaɗu matuƙa da samun labarin mutuwar ƴanwasan, lamarin da ya bayyana da yanayi mai ɗaga hankali da damuwa.
"A madadin gwamnati da al'ummar jihar Kano, muna miƙa ta'aziyarmu ga iyaye da iyali da ƴanuwan waɗanda suka rasu. Sanan ina kira ga dukkan musulmi a jihar da su yi addu'ar samun rahamar Allah ga waɗanda suka rasu."
Gwamnan ya kuma ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen kula da waɗanda suka jikkata, da kuma tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu.
Asalin hoton, Reuters
A yau Lahadi al’ummar ƙasar Poland ke kaɗa ƙuri’a a zazzafan zaɓen shugaban ƙasa, da zai fayyace alƙibilar da ƙasar za ta karkata a nan gaba - walau – ta ci gaba da kasancewa mai bin ra’ayin Turai ko kuma ta koma hannun masu ra’ayin tsattsauran kishin ƙasa.
Za a fafata ne a tsakanin Magajin Garin babban birnin ƙasar, Warsaw Rafal Trzaskowski ChasKovSki da kuma masanin tarihi , Karol Nawrocki a zaɓen na na raba-gardama karo na biyu.
Zaɓen da ake wa kallon na kankankan, zai fayyace ko al’ummar ƙasar sun amince ko kuma sun dawo daga rakiyar tsarin da ake bi yanzu a mulkin ƙasar inda shugaban ƙasa zai iya hawa kujerar-naƙi ya yi watsi da duk wata doka da majalisar dokoki ta yi duk kuwa da cewa majalisar ce ke da yawancin iko a ƙasar– kamar yadda aka gani a ƴan watannin baya inda shugaban ƙasar na yanzu mai ra’ayin riƙau Andrzej Duda, ya hana wata muhimmiyar doka da gwamnatin ƙasar ta haɗaka, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar tarayyar Turai Donald Tusk, ta gabatar.
Asalin hoton, Moscow Interregional Transport Prosecutor's Office
Wata gada ta ruguje a wani yanki na Rasha, kusa da kan iyakar Ukraine, abun da ya sa wasu manyan motoci faɗawa kan wani jirgin fasinja da ke tafiya.
Gwamnan yankin Bryansk Alexander Bogomaz ya ce aƙalla mutum bakwai ne suka mutu sannan sama da talatin suka jikkata.
Wata kafar watsa labaran Rasha da ke kusanci da jami'an tsaro a Moscow ta ce da alama harin zagon ƙasa ne.
Babu wani martani daga Ukraine har kawo yanzu.
Asalin hoton, AP
Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce tun farkon fara gangamin yaƙin neman zaɓen 2023 ne ya yanke shawarar ba zai zaɓi Shugaba Bola Tinubu ba, inda ya ce sun haɗu gaba da gaba, kuma ya faɗa a take cewa shi ba zai zaɓe shi ba.
Amaechi ya ce hakan ya sa ya cika alƙawarin da ya ɗaukar wa kansa na ƙin taimakon yaƙin zaɓen Tinubu, saboda a cewarsa ya gano tun da wuri cewa aikin zai yi wa shugaban nauyi na mulkin Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Amaechi ya bayyana haka ne a wajen taron murnar cikarsa shekara 60 a duniya wanda aka yi jiya Asabar a Abuja.
"A Yola muka haɗu da Tinubu, inda na faɗa masa cewa ni ba zan goya masa baya ba. Kuma ban yi ba, kuma ban zaɓe shi ba. Magana ce ta tunanin ba zai iya ba.
"Wasu daga cikinmu da suke nan ma sun yi zaɓen ne saboda addini da ƙabilanci. Kawai ana wasa da hankalin mutane ne su yi zaɓe bisa la'akari da addini ko ƙabilanci. Kuma ga inda hakan ya kawo mu nan."
Da yake magana game da haɗakar siyasa, Amaechi, "za mu haɗu da jam'iyyun adawa ne idan su ne za su fitar da mu daga cikin ƙangin da muke."
Asalin hoton, Reuters
Hamas da Isra'ila na ci gaba da samun saɓani game da sabon ƙudurin da Amurka ke mara wa baya na tsagaita buɗe wuta a Gaza.
Wakilin na musamman na Amurka a gabas ta tsakiya Steve Witkoff, ya ce matakin da ƙungiyar ta Hamas ta ɗauka na yin gyara ga kundin ba abu ne da za a amince da shi ba.
Ita dai Hamas ta ce za ta saki fursunonin yaƙi huɗu a ranar farko, biyu a rana ta 30, sai kuma huɗu a ranar ƙarshe ta yarjejeniyar, wato rana ta 60.
Ta kuma buƙaci ba da damar shigar da kayan jin-ƙai nan take, tare da yin tayin ajiye shugabancin yankin a siyasance, don ba da damar kafa gwamnatin ƴan takarda, da za ta jagoranci yankin.
Wakiin BBC ya ce buƙatar ƙungiyar ta neman tattaunawar da za ta kai ga kawo ƙarshen yaƙin da kuma janye sojojin Isra'ila baki ɗaya, sun kasance wani batu da ke ci gaba da kawo cikas.
Jama'a barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu cigaba da kawo muku labaran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Ni Isiyaku Muhammed ne zan kasance tare da ku daga nan zuwa wani lokaci.
Ku kasance tare da mu.