Rikicin Trump da Jami'ar Havard ka iya ci gaba har bayan mulkinsa

Bayan Donald Trump ya shafe kwanaki bakwai cikin aiki. A ranar Litinin,ya yi barazanar tura dala biliyan 3 cikin tallafin bincike na Harvard zuwa makarantun koyar da sana'o'i.

A ranar Talata Fadar White House ta aike da wasika zuwa ga hukumomin gwamnatin tarayya, inda ta umurce su da sake nazarin kusan dala miliyan 100 na kwangilolin da gwamnati ta baiwa Harvard da kuma "nemo tallatawa" idan zai yiwu. Akwai 'karin bayanin da zai yi a ranar Laraba game da al'amarin.

"Ya kamata Harvard ta yi gyara," kamar yadda ya shaida wa manema labarai da suka taru a Ofishin shugaban 'kasa. "Harvard bata mutunta 'kasarmu."

Lokacin da aka haɗa da yunƙurin gwamnati - an rufe sama da dala biliyan 3 a cikin tallafin bincike da kuma dakatar da ɗaliban ƙasashen waje shiga Harvard - wannan umarni na Trump ya wakilci duk wani mataki na gaba da za a 'dauka kan shahararrriyar makarantar ta Amurka.

Ko Kotu zata soke wasu daga cikin matakan da aka 'dauka - tuni wasu sun fara tasiri a faɗin manyan makarantun Amurka.

"Kowacce rana suna gabtar da sabbin abubuwa," in ji Greg Wolfson, shugaban ƙungiyar Farfesoshin Jami'ar Amurka. "Amma mai mahimmanci shi ne suna sauya al'adu suna kuma sauya mutane mutane."

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani 'dalibi ya ce Havard zata fuskanci wannan yanayi, to kowacce jami'a ma zata iya fuskanta.

A ranar fara biki a Harvard ranar alhamis, ɗalibai sun ce akwai "damuwa a makaranta" .

Wani wanda ya kammala karatun digiri 'dan Burtaniya wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce "Mutane sun san Trump yana da hannu a wannan yunƙuri, amma [sun yi mamakin] a lokacin da abin ya faru,"

Ya kara da cewa "Idan har hakan zai iya faruwa da Harvard, hakan na iya faruwa ga kowace jami'a a kasar."

Wannan yaƙin tsakanin Harvard da Trump ya yi tsanani. Shin matakan da Trump ke 'dauka zai iya zama kamar yadda wasu ke hasashe cewar yunkurin masu tsattsauran ra'ayi ne na kawar da ginshikan gargajiya da ke goyon bayan jam'iyyar Democrat?

Idan haka ne, harabar jami'ar ta zama dandalin rikici a fagen al'adu da siyasar Amurka.

Zargin ƙyamar Yahudawa

Trump da gwamnatinsa sun ba da bayanai daban-daban game da abin da suka yi, ciki har da rashin masu ra'ayin mazan jiya a cikin manyan malaman Jami'ar Harvard, tare da shawarwarin karbar daliban kasashen waje da yawa da kuma alakar kudi da Chaina.

Sai dai a cewar fadar White House, abin da ya fi daukar hankali shi ne gazawar da jami'ar ta yi wajen nuna 'kyama a cikin harabar jami'ar, bayan zanga-zangar kyamar Isra'ila a jami'o'in fadin Amurka tun bayan fara yakin Gaza.

A cikin watan Disamban shekara ta 2023, fitattun shugabannin jami'o'i uku - ciki har da shugabar Harvard ta lokacin, Claudine Gay - sun yi gwagwarmaya don amsa ko kiran "kisan kare dangi na Yahudawa" ya keta ka'idojin jami'ar lamarin da ya haifar da mummunar suka.

Dr Gay, wanda aka yi wa tambayar a wajen wani taron majalisar dokoki game da 'kyamar Yahudawa a manyan makarantun Amurka, ta amsa cewa ya danganta ne da yanayin da ake ciki. Daga baya ta ba da uzuri, tana gaya wa jaridar ɗaliban: "Lokacin da kalmomi suka rura wutar rikici ba abun da zai biyo baya sai nadama."

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohuwar Shugabar Harvard Claudine Gay

A kan yakin neman zabe a bara, Trump ya yi alkawarin katse tallafin da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejojin da ya ce suna shiga da ya ce suna shiga cikin " farfagandar 'kyamar Yahudawa ". rump na komawa fadar White House a watan Janairu shirin cika alwashin da ya yi.

Jami'o'i da dama - ciki har da Columbia, inda aka gudanar da manyan zanga-zanga- sun amince da aiwatar da sauye-sauye a cikin dokokin tsaron makarantun da kuma sanya ido a sassan ta na Gabas ta Tsakiya da Kudancin Asiya da sashen Nazarin Afirka.

A cikin watan Afrilu, Harvard ta fidda sakamakon wani bincike na jami'a (wanda aka yi kafin zaben Trump) game da ƙyamar baki da 'kyamar musulmi a harabar ta.

Binciken ya gano cewa da dama daga cikin daliban Yahudawa da Musulmi sun fuskanci bambamci da wariya daga manhajar karatun jami'ar.

Duk da haka, bukatun gwamnatin sun wuce kiraye-kirayen magance kyamar Yahudawa.

A cikin wata wasika zuwa ga jami'ar, "Kungiyar hadin gwiwa don ya'ki da 'kyamar Yahudawa" an tsara jerin sauye-sauye da dole ne Harvard ya yi aiki da su, ciki har da dakatar da shirye-shirye daban-daban da sake fasalin shigar 'dalibai da daukar ma'aikata da tantance daliban kasashen waje.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Trump ya yi alkawarin rage kudade a makarantun da suke shiga farfagandar 'kyamar Yahudawa

Tsarin da Trump ya yi amfani da shi da irin matsin lambar da ya ke amfani da ita ta baiwa mutane da dama mamaki a manyan makarantu.

"Ba batun ilimi ba ne," in ji Mista Wolfson. "Karatu a manyan makarantu shi ne ya ke sauya al'ummarmu."

Amma yuwuwar samun sauyi na dogon lokaci zai iya dogara ne akan ko yawancin jami'o'in Amurka sun zaɓi biyan bukatun gwamnati - ko kuma zasu jajirce su ya'ki lamarin, kamar yadda Harvard ke ƙoƙarin yi.

Yaƙin gama gari

Yayin da Harvard ta kasance fitaccen abin da gwamnatin ke sanya a gaba, kuma wadda ta jajirce don kare martabar ta, ɗaya ne kawai daga cikin manyan jami'o'in Amurka da suka samu raguwar kudade ko kuma suke fuskantar da bincike.

Princeton da Jami'ar Pennsylvania sun ba da rahoton cewa gwamnatin ta dakatar da daruruwan miliyoyin daloli a cikin tallafin bincike.

Ma'aikatar Ilimi ta kaddamar da bincike kan jami'o'i 10 bisa zargin kyamar Yahudawa - tare da gargadin wasu da dama da cewa za su iya fuskantar irin wannan bincike.

Har ila yau, tana binciken jami'o'i 52 kan shirye-shiryen da suka danganci wariyar launin fata ba bisa 'ka'ida ba.

Wasu na ganin 'daukar wannan mataki kan manyan makarantu da gwamnatin Trump ta yi abu ne da ya dace a ƙoƙarin sake fasalin jami'o'i .

"A Jami'o'i ba kawai batun ake na neman ilimi ba, batu ne na kawar da masu tsattsauran ra'ayi ," Charlie Kirk, wanda ya kafa kungiyar masu ra'ayin mazan jiya ta Turning Point USA, ya fada a wata hira da Fox News a watan jiya. "zamu girgiza shi."

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Charlie Kirk wanda ya kafa 'kungiyar masu ra'ayin mazan jiya ta Turning Point USA

Mutane da dama daga cikin masu sassaucin ra'ayi sun dade suna kallon manyan makarantun Amurka a matsayin wuraren koyar da ilimin sassaucin ra'ayi, ko a ɗauki tsattsauran ra'ayin.

Kuri'u sun nuna rarrabuwar kai tsakanin waɗanda suka yi karatu kuma ba su halarci kwaleji ba.

A wani bincike na baya-bayan nan da kamfanin zabe Civiqs ya yi, an raba daliban da ba su kammala karatun jami'a ba kan aikin da Trump ke yi a ofis, inda kashi 49% suka ki amincewa da shi, yayin da kashi 47% suka amince.

Wadanda suka kammala karatun kwaleji a 'bangare guda, na da bambanci, ya yinda kashi 58 basu yaba da ayyukan da Trump ya yi a ofis ba da kuma kashi 38 wadanda suka yaba irin rawar da ya taka.

Jami'o'i ne suka janyo wa kansu

A shekarun baya bayan nan a cewar Mista Hess, manyan makarantu na Amurka sun zama masu kusanci da gwamnati da kuma dogaro da kudaden gwamnati.

Ya ce sabuwar tawagar Trump ta dauki nauyin kula da manyan makarantu da binciken kare hakkin jama'a da dokokin yaki da wariyar launin fata da kuma kula da kudade.

Ri'ke kuɗaɗen gwamnatin tarayya daga jami'o'i na iya zama sabon ƙalubale ga manyan makarantu, amma ga masu ra'ayin mazan jiya 'daukar mataki zai dai dai ta

Ci gaba da dakatar da tallafin kudi ga jami'o'i zai zama wani babban kalubale ga bangaren ilmi, amma a wurin wasu wannan wani abu ne kawai daga cikin tsarin 'yan ra'ayin rikau na kawo cikas ga muhimman abubuwa.

Tsare-tsaren da suka shafi sharia a matakin jiha sun haifar da cikas ga ga duk wata hoɓɓasa da lauyoyi ka iya yi domin kawo sauyi ga tsarin dimukuraɗiyya.

Kuma duk wani yunƙuri da zai daƙile ikon gwamnati - wanda ya kai wani babban mataki da ga manufofinElon Musk na rage kashe kuɗi - ya zama wani cikas ga wani tsarin al'ada na Dimukuraɗiyya.

Har ila yau, Mr Wolfson na fargabar cewa ana iya rasa wani muhimmin abu idan har aka ƙaƙabawa jama'a wasu daga tsare-tsaren Gwamnatin Trump.

"Gaskiya ne muna da mutane daga jinsi daban-daban, da al'adu daban-daban, jami'ar da ta haɗa 'yan ƙasashe daban-daban na nufin wani babban abin alfahari ga jami'o'inmu, " in ji shi.

" Hakan zai samar da mabambantan al'adu, kuma hakan ma zai kasance haɗa dangogin masu ilmi wuri ɗaya kenan".

Yadda jami'ar ta mayar da martani

Wataƙila Jami'ar Harvard- wadda ta yi suna a ɓangaren ilmin shari'a - ta rungumi matakin amfani da ƙarfin kotu domin yaƙar matsin lambar da Trump ke yi mata.

A ranar Alhamis, wani alƙalin kotun tarayyar ƙasar ya dakatar da yunƙurin Trump na hana ɗalibai 'yan ƙasashen waje samun takardun biza domin yin karatu a jami'ar.

Jami'ar ta kuma shigar da ƙara domin dakatar da gwamnatin Trump daga tsayar da bayar da tallafin dala biliyan 2.2 a matsayin tallafin karatu, duk da ya ke batun na gaban kotu.

"Yanayin da aka jefa Harvarda da sauran jami'o'i a fili ya ke," kamar Harvarda ta rubuta a cikin ƙorafin da ta shigar a gaban kotun tarayya ta Massachusetts. "aku ba gwamnati damar ruguza cibiyarku ta bayar da ilmi ko kuma ruguza ikon jami'ar na samun nasarori a fannonin binciken kiyyon lafiya da binciken kimiyya da kuma gano sabbin fasahohi ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire".

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuna galibin Amurkawa na goyon bayan jami'o'in ƙasar, kuma ba su amince da tsarin dakatar da ba jami'o'in tallafin kuɗi ba.

A lokacin wata hira da kafar NPR, shugaban Jami'ar ta Harvard, Alan Garber ya kare matakin jami'arsa, inda ya ce Harvarda na nan "daram" ga manufofinta na bayar da ilmi da kuma gaskiya.

"Harvard jami'a ce mai daɗaɗɗen tarihi, da ya girmi ƙasar ma" ya ci gaba da cewa, " Muddin akwai Amurka, to Harvard na da tunanin ci gaba da bautawa ƙasar."

A hannu ɗaya kuma Trump tun da farko ya bayyana ra'ayinsa Harvard dai na saon yaƙar matakin" ya bayyana hakan a ranar Laraba. "Suna son nuna sun da wayo, amma kuma an sa ƙafa an yi fatali da shirinsu."

Wuce gona da iri

Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa matakan da Trump ya ɗauka na amfarnar manufar siyasarsa ne kawai da kuma wata ɓoyayyar manufa.

Kuma wnnan ya nuna galibin Amurkawa na goyon bayan jami'o'in ƙasar kuma ba su amince da rage kuɗaɗen tallafin da ake ba jami'o'in ba.

A wani ɓangare na ra'ayoyin kuma ya bayyana cewa sake jirkita yadda ake tafiyar da tsarin ilmi mai zurfi a Amurka, ko da kuwa an yi amfani da dukan matakai ko dubarun gwamnatin tarayya, to abu ne mai wahalar gaske.

A cewar Mista Wolson, yin kwaskwarima ga abin da ya nema babban naƙasu ne ga 'yancin da ɓanagaren ilmi ke da kuma dole a ƙalubalanci haka.

Da yawa daga Farfesoshi na Ƙungiyar Jami'o'in Amurka na da fargabar sakamakon illar bin ra'ayin siyasa ko gudanar da dun wani bincike maras alfanu.

"Illar a zahiri ta ke", a cewar Mista Wolson. "Ko da kotu ta shigo ciki, an riga an samu babbar illar yadda aka ɗauki kimar ilmi mai zurfi sakamakon aikin ganganci na Trump ."

Mista Hess, mai ra'ayin riƙaua da ya sha yin matsn lamba akan yadda za sake yin tsare-tsare ga ɓangaren ilmi.

Ya yi imanin cewa rigimar Trump da manufofi marasa tsari - ciki har da maganarsa ta makon jiya - za su ƙare ne a matsayin marasa tasiri a maimakon inganta tsarin jami'o'in Amurka.

Wannan duka ba komai ne ba face wani wani buri," in ji Mista Hess. "Ya Allah ko wani mataki ne da zai yi amfani nan gaba, tambaya dai ce da amsarta ke sarari."

Ga alama dole akwai wanda ya ke daidai, har wa yau dai, ko da Amurkawa sun jajirce - ko sun fi ƙarfin yunƙurin Trump, ba dai za su taɓa tsira daga sabon rikicin siyasar Amurka ba.

An keta iyakar inda ƙarfin iko ya tsaya, ya Allah ko dai a samu galaba tsakanin masu keta gaskiya ko kuma masu wanzar da ita - ga a ƙofar.