Ƴanwasa biyar da suka fi taka rawar gani a Champions League

..

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Umar Mikail
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Mabiya harkar wasanni ƙalilan ne - idan ma akwai - suka yi hasashen ƙungiyar Paris Saint-Germain za ta lashe gasar zakarun Turai ta Champions League da aka kammala kafin fara ta.

Ta cinye Inter Milan 5-0 a binrin Munich na Jamus a wasan ƙarshe, wanda masana suka ce shi ne wasan ƙarshe na farko da wata ƙungiya ɗaya ta fi mamaye wasan a tarihi.

Wannan ne karon farko da PSG ta lashe gasar, kuma ta biyu da ta yi hakan daga ƙasar Faransa.

Kakar ta shekarar 2024-25 ta zo da abubuwa da dama, ciki har da sabon salon buga wasannin rukuni, da kuma ƙara yawan tawagogin da ke shiga gasar daga 32 zuwa 36.

A wannan maƙalar mun duba 'yanwasa biyar da suka fi taka rawar gani a gasar.

Ousmane Dembélé

Ousmane Dembélé

Asalin hoton, Getty Images

Ɗanwasan gaba na Paris Saint-Germain, Ousmane Dembélé, shi ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai Euefa ta zaɓa a matsayin mafi hazaƙa a gasar ta Champions League.

Demebele ya kai matsayin ne saboda irin taimakon da ya bai wa zakarun na Faransa ta hanyar jefa ƙwallaye takwas a raga, da kuma bayar da gudummawar cin wasu shida a wasa 15 da ya buga.

Kazalika, shi ne ya fi kowanne ɗanwasa yunƙurin cin ƙwallo a gasar, inda ya kai hari (attempt) sau 64, 23 daga cikinsu akwai munana (on target) 23.

Ya yi nasarar yanka abokan hamayyarsa har sau 62, sannan ya yi bugun kwana 45.

Rapinha

Rapinha

Asalin hoton, Reuters

Ɗanwasan gaba na Barcelona da Brazil, Rapinha, na cikin 'yanwasan da suka fi bai wa mabiya harkokin wasa mamaki a kakar wasa ta bana baki ɗaya - ba a Champions League ba kawai.

Shi da Serhou Guirassy, su ne kan gaba a cin mafi yawan ƙwallaye da 13 kowannensu. Sai dai Rapinha ya zarta shi da yawan bayar da ƙwallo a zira a raga, inda yake 9, Guirassy ke da 4.

Rapinha mai shekara 28 ya ci ƙwallo tara da ƙafarsa ta hagu, uku da dama, da kuma ɗaya da kansa. Huɗu daga cikin ƙwallayen da ya ci daga wajen yadi na 18 ne.

Wani abu da ya kamata a lura da shi shi ne babu bugun finareti ko ɗaya cikin ƙwallayen da ya ci a wasa 14 da ya buga.

Lamine Yamal

Lamine Yamal

Asalin hoton, Reuters

Matashin da ya fi birge 'yankallo ko shakka babu shi ne Lamine Yamal na Barcelona.

Ɗan Sifaniyan mai shekara 17 ya taka rawar gani cikin wasa 13 da hya buga wa ƙungiyar, inda ya kai hare-hare har sau 52. Daga cikinsu akwai munana 25.

Yamal ya ci ƙwallo biyar sannan ya bayar da uku aka zira a raga.

Ya yi nasarar yanka abokan hamayya har sau 109 a gasar, wadda ita ce ta biyu da ya buga wa Barca.

Serhou Guirassy

Serhou Guirassy

Asalin hoton, EPA

Wani ɗanwasan da ya taka rawar gani a kakar da aka kammala shi ne Serhou Guirassy na Burossia Dortmund da kuma Faransa.

Ɗanwasan mai shekara 29 ya jefa ƙwallaye har 13 a raga - iri ɗaya da na Rapinha - sannan ya bayar gudummawa aka ci wasu huɗu cikin wasa 14.

Cikin ƙwallayen da ya ci har da uku rigis ya ɗura wa Barcelona a wasa na biyu na zagayen kwata fayinal.

Harry Kane

Harry Kane

Asalin hoton, Reuters

Ɗanwasan gaba na Bayern Munich kuma kyaftin ɗin Ingila ya ɗora kan abin da ya saba, inda bai gushe ba sai da ya zira ƙwallaye 11 cikin wasa 13 da ya buga wa kulob ɗin.

Kazalika, Kane mai shekara 31 ya kai hare-hare 49, cikinsu akwai masu haɗari 25.

Haka nan, ya bayar da ƙwallo biyu an zira a raga kafin Inter Milan ta yi waje da su daga gasar a zagayen kusa da na ƙarshe.